Da dumi dumi: Gwamna Tambuwal ya bayyana sunan sabon mataimakinsa a Sakkwato
Wani cigaba da aka samu a siyasar jahar Sakkwato itace gwamnan jahar, Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da sunan Alhaji Mannir Dan’iya a matsayin sabon mataimakin gwamnan jahar Sakkwato.
Majiyar Legit.com ta ruwaito sanarwar ta biyo bayan murabus da tsohon mataimakin gwamnan jahar, Alhaji Ahmed Aliyu yayi a ranar 13 ga watan Nuwamba a shirinsa na tsayawa takarar gwamnan jahar Sakkwato a jam’iyyar APC.
KU KARANTA: Ba zan manta da yan Fim, mawaka da yan nanaye ba – Inji Atiku Abubakar
Gwamna Tambuwal ya bayyana sunan Dan Iya ne a ciki wata wasika daya aika ma kaakakin majalisar dokokin jahar Sakkwato, Alhaji Salihu Maidaji inda ya bukaci majalisar ta tantance shi, kuma ta amince da nadinsa a wannan mukami.

Asali: UGC
“Biyo bayan gurbin da ya samu sakamakon murabus na kashin kai da tsohon mataimakin gwamnan jahar, Ahmed Aliyu yayi, ina sanar da kai sunan Alhaji Mannir Dan’ya a matsayin sabon mataimakin gwamna duba da sashi na 191 (3) (c) na kundin tsarin mulkin Najeriya, ina bukatar majalisar ta amince da shi.” Inji Tambuwal a cikin wasikar.
Kaakakin majalisar ne ya karanto wannan wasika a yayin zaman majalisar na ranar Laraba 21 ga watan Nuwamba, inda bayan kammala karatun wasikar sai duka yan majalisar suka amince da sanya ranar 22 ga watan Nuwamba don tantance Mannir Dan’iya.
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wammako ya bayyana ma uwar jam’iyyar APC cewa kada ta damu, zai kwato duka kujerun siyasa dake jahar Sakkwato, tun daga kan gwamna har kansila a zaben 2019.
Sanata Wamakko, ya bayyana haka ne a gidansa dake unguwar gawon nama cikin garin Sakkwato yayin dayake gabatar da jawabi ga taron jiga-jigan yayan jam’iyyar APC jim kadan bayan dawowarsa daga babban birnin tarayya Abuja, inda yace Buhari da sauran yan takarar APC za suyi nasara a 2019.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng