Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan Mutane 53 a Arewacin Najeriya

Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan Mutane 53 a Arewacin Najeriya

Mun samu cewa kimann rayukan soji da manoma 53 ne suka salwanta cikin kwanaki uku kacal sakamakon aukuwar hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya kamar yadda majiyoyin rahoto na hukumomin tsaro suka bayyana.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito sun bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ta kara kaimi wajen zartar da hare-hare domin bayyana karfin ikonta ga gwamnatin kasar nan yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da karatowa.

Duk da ci gaba da ikiraran gwamnati na sauran kiris ta kawo karshen wannan kungiya a kasar nan, kungiyar a kwana-kwanan nan ta zartar wasu munanan hare-hare kan hukumomin tsaro da kuma al'umma.

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ci gaba da hankoron sake neman zaben kujerarsa a babban zabe da za a gudanar a watan Fabrairu na badi, ya na kuma ci gaba da fuskantar kalubalai da korafe-korafen musamman dangane da yanayi na rashin tsaro.

Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan Mutane 53 a Arewacin Najeriya
Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan Mutane 53 a Arewacin Najeriya
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, aukuwar wani mummunan hari na kungiyar ta'adda ta Boko Haram a karshen makon da ya gabata ya salwantar da rayukan dakaru 43 cikin wasu sansanin su na Metele daf da gabar kasar Nijar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

KARANTA KUMA: Gwamna Dickson ya bayar da gudunmuwar N100m ga Gidauniyar tsohon shugaban kasa Jonathan

Kazalika rahotanni sun bayyana cewa, 'yan ta'adda sun yi awon gaba da wasu Mata 7 yayin da suke tsaka da gudanar da aikace-aikacen gona a garin Bama da ke jihar Borno.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kimanin rayukan mutane 27, 000 sun salwanta tun yayin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da ta'ddancinta cikin kasar nan a shekarar 2009 da ta gabata baya ga kimanin Mutane 1.8m da suka rasa muhallansu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng