An yi bikin Mauludi mai kayatarwa a Bauchi, hotuna
A yau Talata 20 ga watan Nuwamba ne al'ummar musulmi a fadin duniya ke bukin Mauludi wadda akeyi domin zagoyar ranar haihuwan Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW).
Suma al'ummar Najeriya ba a bar su a baya ba wajen murnar zagowar wannan rana mai muhimmanci domin suna gudanar da wa'azozi da shagulgula daban-daban a duk lokacin da ranar ta zagayo.
Kamar yadda aka saba, al'ummar musulmi su kanyi tattaki a manyan titunan birane da kauyuka sanya kayayaki masu kayatarwa suna rera wakokin yabo da bege ga manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW).
Wannan karon ma dandazon al'ummar jihar Bauchi sun fito kwansu da kwarkwata domin murnar zagoyawar wannan rana mai albarka da muhimmanci.
Ga dai hotunan yadda Maulidin ya kasance a garin Bauchi kamar yadda muka samu daga Daily Trust.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: An kashe mutane, an kona gidaje da mota a wani biki a jihar Bauchi

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A sakonsa na Mauludi wannan shekarar, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kasar na bukatar hadin kai da addu'oi domin al'ummar kasar su shawo kan kallubalan da ke adabarsu.
A sakon da ta fito daga hannun hadiminsa kan yada labarai, Garba Shehu, shugaban kasa ya mika sakon murnarsa ga dukkan musulmi da ke gida Najeriya da kasashen waje.
Ya kuma bukaci su taya kasar da addu'a na ganin cewa an gudanar da zabe lafiya tare da samun cigaba a kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng