Sojojin Najeriya kadai ba zasu iya gamawa da Boko Haram ba - Buhari
- Shugaba Buhari ya bayyana cewar dakarun sojin Najeriya kadai ba zasu iya kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram ba
- Buhari ya ce akwai bukatar hadin kai tsakanin hukumomin tsaro, ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati domin kawo karshen aiyukan mayakan kungiyar Boko Haram
- Kazalika shugaba Buhari ya yabawa hukumar sojin sama bisa shirya taron da ta yi domin yin bita da fadakar da jami'anta a kan salo da dabarun yaki da 'yan ta'adda
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar dakarun sojin Najeriya kadai ba zasu iya kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram ba.
Kazalika, Buhari ya bayyana siyasa a matsayin abinda ya fara kawo matsalar Boko Haram a Najeriya.
Buhari ya bayyana cewar akwai bukatar hadin kai tsakanin hukumomin tsaro, ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati domin kawo karshen aiyukan mayakan kungiyar Boko Haram.

Asali: Depositphotos
Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi a wurin wani taron hukumar sojin sama da aka gudanar yau, Litinin, a Abuja.
Da ya ke bayyana takaicinsa bisa halin rashin tsaro, shugaba Buhari ya bukaci dukkan 'yan Najeriya su rungumi canji na gaskiya da zai tabbatar da tsaro a salon mulkin farar hula.
DUBA WANNAN: Dakarun soji sun kashe jami'in watsa labarai na kungiyar Boko Haram, hotuna
"Matukar ana bukatar yin nasara a kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram dole hukumomin tsaro da ma'aikatun gwamnati daban-daban su bawa sojojin Najeriya hadin kai ta fuskar samar da bayanai da yin aiki tare domin cimma mamufa daya," a cewar Buhari.
Sannan ya kara da cewa, "duk da muna bukatar sojoji domin yaki da aiyukan ta'addanci, ba za a samu nasara ba sai an ba su hadin kai saboda tushen rikicin na da alaka da siyasa."
Kazalika shugaba Buhari ya yabawa hukumar sojin sama bisa shirya taron da ta yi domin yin bita da fadakar da jami'anta a kan salo da dabarun yaki da 'yan ta'adda.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng