An kashe mutane, an kona gidaje da mota a wani biki a jihar Bauchi
- Fada ya kaure tsakanin wasu matasa a wajen bikin zagayowar ranar haihuwa a jihar Bauchi
- An kashe mutane uku, an kona gidaje biyu da mota guda daya tare da jikkata mutane da dama
- Jami'an 'yan sanda sun hallarci inda abin ya afku kuma sun kama mutane 75 da ake zargi da hannu cikin tayar da rikicin
A kalla mutane uku ne suka rasu yayin tare da kona gidaje biyu da mota guda a safiyar Litinin a yayin da fada ya kaure tsakanin wasu matasa da suka hallarci wata biki a jihar Bauchi kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
Wasu da suka bayar da sheda a unguwar Yelda da ke Bauchi sun ce sun farka daga barci ne yayin da suka ji karar harbin bindiga misalin karfe 11 a dare.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Saraki ya fadi gwamnonin APC biyu da ke fuskantar wulkanci a jam'iyyar
"Karar harbin yana da kara sosai kuma an kwashe sa'o'i ana harbe-harben sannan daga baya mu ka ji sahun gudun mutane," inji wani mai shagon trader da ya ce sunansa Mr Mathew.
"Daga baya mun gano cewa yan sanda da sojoji da aka kira domin kwantar da tarzomar ne suka rika harbe-harben.
"Mun gano cewar wasu mutane sun rasa rayyukansu sakamakon fadan," inji shi.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar, DSP Kamal Datti ya shaidawa Premium Times ya ce a halin yanzu an kama mutane 75 da ake zargi da hannu cikin afkuwar rikicin.
Mr Datti ya kuma tabbatar cewa an rasa rayyuka sakamakon rikicin.
"Abinda ya faru shine a daren jiya wasu matasa sun shirya bikin murnar zagayowar ranar haihuwa a unguwar Lushi inda daga baya rikici ya barke tsakanin wasu matasan da suka hallarci bikin.
"Sakamakon fadan ya kaure, mutane uku sun rasa rayyukansu, an kone gidaje biyu da mota guda daya yayin da wasu mutane biyar sun jikkata," inji Datti.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng