2019: Kungiyar direbobin Keke Napep sun bayyana goyon bayansu ga Buhari a kyautar Mota
Kungiyar direbobin Keke Napep sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2019 inda Buhari ke neman zarcewa akan mukaminsa na shugaban Najeriya.
Legit.com ta ruwaito kungiyar ta bayyana goyon bayan nata ne tare da jaddadashi a ranar Lahadi, 18 ga watan Nuwamba a yayin wata ziyara da suka kai babbano ofishin yakin neman zaben Buhari dake Abuja.
KU KARANTA: Zargin kisan kai: Obasanjo ya maka wani dan jarida gaban Kotu da neman naira biliyan 1

Asali: Facebook
A yayin kwarya kwaryan taron, yayan kungiyar sun bayyana ma wakilin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, kaakakin shugaban kasa Buhari, cewa suna tare da Buhari dari bisa dari, sa’annan suka mika masa kyautar sabuwar mota kirar Toyota Tundra SUV don amfanin kungiyar yakin neman zaben Buhari.
Idan za’a tuna a kwanakin baya ne kungiyar kwandosta ta Najeria ta bayyana goyon bayanta ga shugaba Buhari don neman zake darewa mukamin shugaban Najeriya a zaben shekarar 2019, inda suka yi alkawarin bashi kuri’u miliyan goma.
Kungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar goyon bayan Buhari ne saboda mutuncin da yake da shi a idonsu fiye da sauran yan takarkarun dake neman mukamin shugaban kasar Najeriya.

Asali: Facebook
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ma yan Najeriya wasu sabbin ayyuka da yayi alkawarin gudanarwa a zangon mulki na biyu idan har suka sake zabarsa a karo na biyu.
Buhari ya bayyana hake ne a wani taron kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyu daya gudana a fadar shugaban kasa kuma ya samu halartar gwamnoni goma sha daya, Sanatoci, manyan jami’an gwamnati da jiga jigan yan siyasa.
A yayin jawabin nasa, Buhari ya dauki alkwarin yin garambawul ga fannin ilimin Najeriya gaba daya, inda yayi alkawarin gayara makarantu guda dubu goma a duk shekara, a shekaru hudu masu zuwa zai gyara makarantu dubu arba’in kenan don su zama daidai dana zamani.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng