Sabon alkawari: Buhari zai sake makarantu dubu goma a duk shekara idan ya zarce

Sabon alkawari: Buhari zai sake makarantu dubu goma a duk shekara idan ya zarce

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ma yan Najeriya wasu sabbin alkawurran daya dauki alwashin cika musu matukar suka bashi damar sake zarcewa akan mukamin shugaban kasar Najeriya.

Legit.com ta ruwaito Buhari ya bayyana hake ne a wani taron kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyu daya gudana a fadar shugaban kasa kuma ya samu halartar gwamnoni goma sha daya, Sanatoci, manyan jami’an gwamnati da jiga jigan yan siyasa.

KU KARANTA: Kowa ya debo da zafi: Wani Uba ya yi ma mutumin da yayi ma diyarsa fyade dandaka

A yayin jawabin nasa, Buhari ya dauki alkwarin yin garambawul ga fannin ilimin Najeriya gaba daya, inda yayi alkawarin gayara makarantu guda dubu goma a duk shekara, a shekaru hudu masu zuwa zai gyara makarantu dubu arba’in kenan don su zama daidai dana zamani.

Haka zalika Buhari ya yi alkawarin horas da malaman dake koyarwa a wadannan makarantu akan dabarun koyarwa na zamani ta yadda zasu baiwa dalibansu igantaccen ilimi, musamman ilimin kimiyya da fasaha.

Bugu da kari shugaba Buhari ya jaddada manufarsa ta cigaba da yaki da cin hanci da rashawa ganga ganga, inda yace “Mun sani kafin mu samu nasara sai mu nada mutunci, kima da daraja, musamman a tsakanin shuwagabannin Najeriya da talakawanta.

“Rashawa na muguwar barazana ga cigaban Najeriya, duk da kokarin da muka yin a garkame kofar rashawa a Najeriya, mun sani akwai sauran aiki a gabanmu, a shirye muke mu fadada aikin da muka fara a baya ta yadda zamu ririta arzikin kasa domin amfanin yan kasa gaba daya.” Inji shi.

Bugu da kari Buhari ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru uku da rabi da ta kwashe bisa mulki. “A shekaru hudu da suka gabata mun yi ma yan Najeriya alkawarin canji a yadda ake tafiyar da gwamnati, kuma munyi kokari matuka wajen tabbatar da wannan alkawari.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng