INEC ta saki sakamakon zaben maye gurbi a jihar Kwara
A daren jiya, Asabar, ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaben maye gurbi na kujerar majalisar wakilai ta mazabar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero.
Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abimbola Adesoji, baturen zabe na hukumar INEC, ya bayyana cewar APC ta samu kuri'u 21,236 yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 18,095.
Ya kara da cewar Labour party ta samu kuri'u 150, jam'iyyar PPN ta samu kuri'u 76, sai kuma jam'iyyar UPN da ta samu kuri'u 42.
Farfesa Adesoji ya ce an kada jimillar kuri'u 40,930 a zaben, adadin kuri'u 1,331 ne su ka lalace.
A jiya, Asabar, ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da zaben maye gurbin wasu kujeru daban-daban a jihohin Bauchi, Katsina, Kwara da Kuros Riba.

Asali: Depositphotos
Rahotanni sun bayyana cewar ma su zabe a jihar Kwara sun fito kwan su da kwarkwata domin kada kuri'a a zaben maye gurbin majalisar wakilai a mazabun Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero.
DUBA WANNAN: Kamfen: PDP ta shiga damuwa a kan tunkarar yankin kudu maso yamma
A mazabar Oro ta 2, inda ministan yada labarai na kasa, Alhaji Lai Mohammed, ya kada kuri'ar sa, ga yadda sakamakon zaben ya kasance;
APC 138
PDP 49
A wani sakamakon kuma da aka saki, dan takarar jam'iyyar PDP ya fadi akwatinsa a mazabar sa. Ga sakamakon:
Igangu Alatise
APC 120
PDP 80
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng