Matsawar da mata ta ke yi min ya saka ni fashi - Dan fashi ya fadi labarinsa

Matsawar da mata ta ke yi min ya saka ni fashi - Dan fashi ya fadi labarinsa

- Wani magidanci mai shekaru 38 mai suna Ibrahim Kazeem ya amsa cewa shine jagoran wata kungiyar 'yan fashi da makami guda hudu

- Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Kazeem da 'yan kungiyarsa sun kware wajen yiwa mutane duka sannan suyi fatalli da su daga cikin motar da ke tafiya

- Bayan an damke shi a Legas ya fadawa 'yan sanda cewar bani-banin matarsa ne ya saka shi fadawa mummunan sana'ar fashi da makami

Wani mutum mai suna Ibrahim Kazeem mai shekaru 38 da haihuwa ya fada komar 'yan sanda a jihar Legas bisa zarginsa da aikata fashi da makami. Wanda ake zargin ya shaidawa 'yan sanda ya fara fashi da makami ne saboda tsananin matsin da matarsa ke masa na tambayarsa kudi.

Bayan da aka kama shi a jihar Legas a cikin kwana kwanan nan, Kazeem ya amsa cewa sukan kaiwa mutane hari sannan su kwace kayayakinsu tare da wasu abokansa guda hudu. Rahotanni sun bayyana cewa Kazeem da sauran yan fashin sukan turo mutane daga mota shi bayan sunyi musu fashi.

Mata ta ce ta sanya na fara fashi da makami
Mata ta ce ta sanya na fara fashi da makami
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Ba sa rabawa da mu - Saraki ya fadi dalilin samun sabani da Buhari

A wata hira da akayi dashi, Kazeem ya ce: "Ni babba a gidan mu kuma iyayen mu sun mutu. Daya daga cikin kanai na yana 500 level a jami'a inda ya ke karanta Industrial Chemistry. Daya kuma yana makarantar sakandire sannan biyu suna koyan sana'ar hannu a Legas; Ni nake kulawa da su.

"Na fara samun matsaloli ne bayan na auri mata ta. Ta haifa min yara amma ba ta yi min biyaya. Sai dai kullum ta rika damu na bani-bani har abin ya fara fin karfi na. A maimakon da rika hakura da abinda na ke dashi sai ta rika hangen abinda ya fi karfin ta. Sa da yawa tana fada min in tafi in nemo kudi kamar yadda sauran maza ke nemowa.

"Akwai wani sabulu da nayi asiri da shi na kuma fada mata cewa idan ta sake ta taba zan mutu. Bayan na tafi aiki sai ta dauki sabulun ta lalata shi, a lokacin ne na gane cewa bata kauna ta kuma za ta iya kashe ni, wannan da kuma yawan tambaya na kudi da ta keyi yasa na ce ta bar min gida na."

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wasu jami'an yan sanda a jihar Ogun sunyi zanga-zanga saboda rashin muhalli da ba su dashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel