Abubuwan da kasar Jamus ke bukata kafin ta bawa dan Najeriya bizar shiga Turai

Abubuwan da kasar Jamus ke bukata kafin ta bawa dan Najeriya bizar shiga Turai

- Kasar Jamus ta saki jaddawalin yadda zaka iya ziyartar ta

- Sai dai kowacce kasa za'a je sai an je da visa daga gida

- Da yawan 'yan Najeriya suna son zuwa Turai yawo

Abubuwan da kasar Jamus ke bukata kafin ta bawa dan Najeriya bizar shiga Turai
Abubuwan da kasar Jamus ke bukata kafin ta bawa dan Najeriya bizar shiga Turai
Asali: Facebook

Duk da yawan 'yan Najeriya masu son ballewa suje yawo kasashen waje, musamman masu bi ta ruwa da sahara, kasashen duniya sunyi amanna cewa masu ilimi daga Najeriya, suna taimakawa sosai wajen ci gaban manyan kasashen duniya.

Don ko a Amurka ma, an tabbatar 'yan Najeriya sun fi kowa yiin karatun Boko, sun kuma fi kowanne baqo a kasar kokari a makaranta, da neman na kai.

Yanzu dai Jamus ta saki jaddawalin ababen da mutum zai bukata muddin zai je mata kasa ko yawon shakatawa ko kuma zama na din-dindin.

DUBA WANNAN: Dangote zai dauki sabbin ma'aikata

1. Sai ka bada takardun banki, an tabbatar kana da kudi ajiyayyu a banki

2. Takardun shaidar kana aiki a kasar ka

3. Takardun Passpo, da visa daga ofishin jakadancin kasashen kan baka damar zuwa

4. Hoto dan karami

5. In karatu ne, shaidar ka iya jamusanci

6. Rasit na biyan kudin yin bizar

7. Shaidar byan kudin jirgi, zuwa da dawowa, Otal da na abinci.

8. Katin banki na bashi, mai kamar ATM, wanda kaka iya amfani dashi a can.

9. Shaidar allurar riga-kafi daga cututtuka.

10. Takardun Inshora.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng