Wasu motocin yakin neman zaben Shugaba Buhari za su fara yawo a Gari

Wasu motocin yakin neman zaben Shugaba Buhari za su fara yawo a Gari

Yayin da ake fara shiryawa zaben 2019 gadan-gadan, mun samu labari a karshen makon nan cewa an fara ganin motoci da hotunan yakin tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin Jihar Legas.

Motocin yakin neman zaben Shugaba Buhari za su fara yawo a Gari
Motocin kamfen din Buhari na 2019 sun fara barin Legas
Asali: UGC

A Ranar Lahadin nan ne za a soma fafatukar yakin neman zaben 2019 inda ake ganin za a gwabza tsakanin Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP mai adawa da kuma Shugaba Muhammadu Buhari a bangaren Jam’iyyar APC mai mulki.

Kamar yadda labari ya zo mana, a jiya Alhamis, 16 ga Wata da sassafe ne aka soma ganin motocin yakin neman zaben Buhari su na yawo a cikin Legas. An ga motoci kusan 100 da tambarin Jam’iyyar da hotunan Shugaba Buhari a kan titi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi magana kan bidiyoyin zargin cin hancin Ganduje

Wasu motocin yakin neman zaben Shugaba Buhari za su fara yawo a Gari
Motocin yakin neman zaben Buhari sun baro Legas
Asali: UGC

An ga motoci rututu samfurin Hyundai H1 ta kirar 2009 ne a kan hanyar Legas zuwa Garin Ibadan a daidai gabar Magodo-Berger. Wadanda su ka ga motocin a kan hanya, sun tabbatar da cewa ana fita da su ne Legas zuwa wasu Jihohin.

Jaridar Information Nigeria tace irin motar sabuwa a leda ta kan kai Naira Miliyan 7 yayin da gwanjon su kuma kai kai Naira Miliyan 2.5 zuwa 3.0. Wannan dai ya nuna cewa Jam’iyyar ta APC ta shiryawa zaben da za ayi a farkon 2019 da kyau.

Dazu kun ji cewa kwamitin yakin neman zaben Atiku sun yi wani zama kwanan. Yan takaran na PDP sun yi taro ne da Rabiu Kwankwaso da Bukola Saraki da wasu Gwamnonin Jam'iyyar game da zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel