Wani dan majalisa ya sake ficewa daga APC, ya bayar da dalilai
- Dan majalisar dokoki na tarayya daga jihar Niger, Ahmed Abu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress APC
- Abu ya bayyana cewa rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zabukkan cikin gida na jam'iyyar ce dalilin ficewarsa
- Dan majalisar ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta bayyana sunan wani dan takara a matsayin wanda ya lashe zaben da ba a kammala ba
Dan majalisa mai wakiltan, yankunnan Mokwa/Lavun/Edati na jihar Niger, Ahmad Abu ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC) saboda karya wasu dokoki da ya yi ikirarin anyi a yayin gudanar da zabukkan cikin gida.
A wasika mai dauke da sa hannunsa da ya aike wa mataimakin ciyaman din APC na Arewa ta Tsakiya, da Ciyaman din APC na Niger da kuma Ciyaman din mazabarsa, ya bayyana cewa bai gamsu da sakamakon zabukan da aka gudanar a ranar 4 ga watan Oktoba a Niger.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi
Dan majalisar ya ce an samu tashe-tashen hankula da rashin bin dokokin zaben wadda hakan yasa aka soke zaben amma abin mamaki shine daga baya jam'iyyar ta mika sunnan wani dan takara ga hukumar INEC a matsayin wanda ya lashe zaben.
Abu ba shine mutum na farko da ya fice daga jam'iyyar ta APC ba bisa zargin rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zabukkan cikin gida na jam'iyyar da akayi a watan Oktoba.
A baya, Legit.ng Hausa ta kawo muku cewa Sanata mai wakiltan Niger ta Kudu, Sani Mustapha Mohammed shima ya yi murabus daga APC saboda rashin gamsuwa da zaben cikin gidan.
Mohammad ya yi fushi ne saboda matakin da jam'iyyar ta dauka na cire sunansa daga cikin jerin sunayen yan takarar da aka tantance domin fafatawa a zaben 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng