Rundunar Sojan kasa ta aika da sabbin dakarun Soji na musamman zuwa Borno

Rundunar Sojan kasa ta aika da sabbin dakarun Soji na musamman zuwa Borno

Babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya tura da sabbin dakarun Sojojin Najeriya na musamman zuwa filin daga dake yankin Arewa maso gabas, kamar yadda jaridar Legit.com ta ruwaito.

Manufar tura wadannan dakaru na musamman Arewa maso gabas shine don su fafata da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, musamman a jahar Borno domin a samu nasarar kawo karshen yaki da ta’addanci.

KU KARANTA: Gwamnati ta tanadi hukuncin wata 6 a kurkuku ga duk wanda ya boye man fetir

Rundunar Sojan kasa ta aika da sabbin dakarun Soji na musamman zuwa Borno
Rundunar Sojan kasa
Asali: Facebook

Dakarun Sojin sun tafi ne dauke da kayansu, da kuma manyan makamai da zasu taimaka musu wajen yakar mayakan yan ta’addan, wadanda a yanzu haka suke cigaba da kai farmaki a garuruwa daban daban na jahar Borno.

A wani labarin kuma, runduna ta 82 na sojin Najeriya ta gudanar da atisayen nuna karfi a jahar Abia, da Anambra, Kuros Riba, Enugu, da Imo kamar yadda shugaban rundunar sojojin kasa, Tukur Yusuf Buratai ya umarta.

Rundunar ta yi haka ne domin tabbatar ma jama'an jahohin cewa hukumar ta shirye atisayen ne don bayyana shirinsu na maganin duk wani kalubalen tsaro da taso a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu ke fuskanta.

Rundunar Sojan kasa ta aika da sabbin dakarun Soji na musamman zuwa Borno
Rundunar Sojan kasa
Asali: Facebook

A jawabin kwamandan rundunar soji ta 82, Manjo Janar Emmanuel Kabuk, ya bayyana cewa an gudanar da atisayen ne lokaci guda a jihohin daban-daban, sa’annan ya kara da cewa atisayen ba wai anyi atisayen bane don wani mutum ko kungiyar mutane.

“An yi shi ne domin aika sako ga duk ma su niyyar tayar da hankalin jama'a don su sani cewa hukumar Soji ba zata saurara musu ba.” Inji shi

Mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanal Sagir Musa, ya bukaci jama'a dasu cigaba da harkokinsu tare da bukatar su sanar da hukuma duk wani lamari da kan iya kawo fitina ko tashin hankalin jama'a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng