Hadakar rundunar soji ta gudanar da atisayen nuna karfi a jihohin kudu 4
Rundunar sojin Najeriya ta 82 tare da hadin gwuiwar wasu jami'an tsaro sun gudanar da atisayen nuna karfi a jihohin Abiya, Anambra, Kuros Riba, Enugu, da Imo.
Rundunar ta gudanar da atisayen ne bisa umarnin shugaban rundunar sojoji, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, domin tabbatar wa da jama'a cewar hukumar soji a shirye ta ke ta yi maganin duk wani kalubalen tsaro da yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu ke fuskanta.
A jawabinsa, Manjo Janar Emmanuel Kabuk, kwamandan rundunar soji ta 82 ya ce an gudanar da atisayen ne lokaci guda a jihohin daban-daban.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Sannan ya kara da cewa atisayen ba a yi shi don wani mutum ko kungiyar mutane ba, an yi ne domin aika sako ga duk ma su burin tayar da hankalin jama'a don su sani cewar hukuma ba zata saurara ma su ba.
DUBA WANNAN: Babu wanda ya kama ni, karya ce kawai irin ta fadar shugaban kasa - Sanatan APC
Kanal Sagir Musa, mataimakin darektan hulda da jama'a na hukumar soji, ya bukaci jama'a da su cigaba da harkokinsu tare da bukatar su sanar da hukuma duk wani lamari da kan iya kawo fitina ko tashin hankalin jama'a.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng