Jonathan ya nada Buhari bako na musamman a taron da ya gayyaci su OBJ da IBB
- Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai kaddamar da wani littafi a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai kasance bako na musamman a wurin kaddamar da littafin mai taken "My Transition Hours"
- Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ne zai kasance uban taron da ake sa ran tsofin shugabannin kasa da gwamnoni za su halarta
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sanar da cewar zai kaddamar da littafin da ya rubuta mai taken "My Transition Hours" a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba.
A sanarwar da ya fitar, Jonathan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai kasance bako na musamman a wurin taron kaddamar da littafin.
Legit.ng ta gano cewar za a yi taron kaddamar da littafin ne a Otal din Transcorp Hilton da ke birnin tarayya, Abuja.

Asali: UGC
A shekarar 2015 ne Jonathan ya mika mulkin Najeriya a hannun Buhari bayan ya amince da kayen da aka yi masa a zabe.
A yau, Talata, ne Jonathan ya sanar da batun kaddamar da littafin a shafinsa na Tuwita tare da sanar da cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai kasance uban taro.
DUBA WANNAN: Badakalar biliyan N5.7bn: Tsohon hadimin Shema ya kwance ma sa zani a gaban kotu
Manyan bakin da ake sa rai za su halarci taron kaddamar da littafin sun hada da tsohon shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama; tsofin shugabannin Najeriya: Yakubu Gowon, Ibrahim Badamasi Babangida IBB), Abdulsalami Abubakar, da kuma dan takarar shugaban kasa a tutar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Tsohon alakalin alkalan Najeriya, Jastis Alfa Belgore, ne zai yi bitar littafin, sannan tsohon ministan tsaro, Theophilus Yakubu Danjuma, ya gabatar da shi.
Sarkin Onitsha, Igwe Alfred Nnaemeka Achebe, ne zai kasance babban basarake a wurin taron.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng