Wata mata ta roki kotu kar ta kashe ma ta aure bayan ta nemi a raba aurenta da mijinta

Wata mata ta roki kotu kar ta kashe ma ta aure bayan ta nemi a raba aurenta da mijinta

Wani abin mamaki ya faru a ranar Talata a wata kotu da ke zamanta a Mapo a Ibadan inda wata matar aure mai yara biyu, Beauty Odinye ta dawo kotun ta roki a ayi watsi da bukatar da ta shigar da fari ne neman a raba aurenta.

Ta roki kotun tayi watsi da shaidar da ta bayar na cewar mijinta, Nathaniel yana fama da matsalar yasa ba zai iya mata ciki ba da kuma rashin kulawa da ita.

Beauty ta shaidawa kotu cewar yaran da ta haifa guda biyu ma ba na mijinta bane, yaran wani saurayinta ne mai suna Adedeji Ishola da ta ke zina da shi yayin da ta ke da aure.

Wata mata ta roki kotu kar ta kashe ma ta aure bayan ta nemi a raba aurenta da mijinta
Wata mata ta roki kotu kar ta kashe ma ta aure bayan ta nemi a raba aurenta da mijinta
Asali: Twitter

Nathaniel wanda dan kasuwa ne ya musanta zargin cewar yana da matsalar na haihuwa.

DUBA WANNAN: Kungiyar CAN ta tsoma baki cikin rikicin El-Rufai da Obi

Kotun ta umurci Beauty ta gabatar da saurayinta da tayi ikirarin shine mahaifin yaranta sai dai ta gaza cika wannan umurnin a zaman na biyu da kotun tayi.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa Nathaniel ya bukaci kotun ta bashi izinin rike yaransa biyu tunda matar ta gaza gabatar da wanda ta ce shine mahaifin yaran a gaban kotu.

Sai dai wani abin mamaki shine yadda Beauty ta bayyana a kotu ranar Talata ta tsuguna tana rokon gafarar mijinta Nathaniel tana mai cewa ta janye maganar da ta fadi da farko na cewar yaran da ta haifa ba nasa bane.

"Karya nayi lokacin da nace mijina ba shine mahaifin yara na biyu ba. Ban san abinda ya same ni a lokacin ba," Beauty ta roki kotu.

Sai dai Nathaniel ya ki amincewa ta wannan tubar na matarsa inda ya ce ta bata masa suna kuma ta kunyatta shi a gari.

Shugaban kotun, Chief Ademola Odunade ya bukaci ma'auratan biyu da yan uwansu zuwa ofishinsa domin yin sulhu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164