Yadda wata soja ta sheke dan sanda da mari bayan ya kawo mata wargi
Wani jami'in dan sandan Najeriya ya debo ruwan dafa kansa bayan ya kira wata mace 'karuwa' a Legas alhalin bai san cewa matar jami'an sojan Najeriya ce mai mukamin Kanar.
A cewar wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta na Twitter mai suna Uche Odege Mondial (@ucheodege), matar da shararawa jami'in dan sandan mari mai shiga jiki sakamakon fada mata kalman batancin.
Kuma bayan ta bayyana masa ko ita wacece, dan sandan da abokansa sunyi ta bata hakuri kan abinda su kace subutan baki ne.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: An rufe wata makaranta a kudancin Najeriya saboda wasu dalibai sun saka Hijab
Ga abinda Odege ya rubuta: "Wasu 'yan sanda sun tsayar da wani mutum da budurwarsa. Sai suka bukkaci su nuna musu katin shaida da zai bayyana ko su wanene. Sai daya daga cikin yan sandan ya fadawa yan uwansa cewa matar ba za ta iya bayyana wani katin sheda ba saboda "karuwa ce". Matar dai ba ta ce komai ba.
Sai na matsa kusa da 'yan sandan na fada masa cewa na san wani da ke aiki tukuru domin ganin cewa an kawo gyara cikin aikin 'yan sanda. Dan sandan ya tambaye ni shin ko Sega ne? Sai matar ta ce min wannan ba batun sega bane.
A lokacin ne na gane cewa dan sandan da matar duk sun san Sega.
Kwatsam kawai sai naji karar mari da fuskan dan sandan. Sannan sai ta fada masa cewa ita Kanar ne a Soja. Na tafi na bar yan sandan suna bata hakuri bisa abinda suka fadi a kanta."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng