Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ma Sarkin Kano ziyara cikin dare (Hotuna)
Mai girma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ma mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ziyarar girmamawa a fadarsa dake birnin jahar Kano, kamar yadda Legit.com ta samu tabbataccen rahoto.
Sanata Kwankwaso ya kai wannan ziyara ne a cikin daren Lahadi 11 ga watan Nuwamba tare da rakiyar dan takarar gwamnan jahar Kano a jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa Aminu Abdulsalam Gwarzo.
KU KARANTA: Babban bankin Najeriya ta bayyana wadanda suka fi taurin bashi tsakanin Maza da Mata

Asali: Facebook
Sauran wadanda suka taka ma tsohon gwamnan baya sun hada da yan takarkarun kujerun Sanatoriyan jahar Kano guda biyu, da sauran jiga jigan na hannun damansa, kamar yadda hotunansu suka bayyana.
Tun bayan shan kayin da yayi a hannun Atiku Abubakar a zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP inda ya zama na hudu ne aka daina jin duriyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Facebook
A zaben fidda gwanin daya gudana a garin Fatakwal na jahar Ribas, Rabiu Kwankwaso ya samu kuri’a 158 kacal, wanda hakan ya bashi damar tsayawa a mukami na hudu a bayan Atiku Abubakar mai kuriu 1,532, Aminu Waziri Tambuwal 693 da Bukola Saraki mai kuriu 317.
Sauran yan takarkarun sun hada da Jonah Jang mai kur’u 19, Datti Ahmed kuri’u 5, David Mark mai kur’u 35, Tanimu Turaki kuri’u 65, Sule Lamido kuri’u 96, Attahiru Bafarawa kuri’u 48, Ibrahim Dankwambo kuri’u 111, da Ahmed Makarfi kuri’u 74.

Asali: Facebook
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng