Mun samu labari cewa Gwamnatin Buhari ta na neman ganin bayan Atiku – Inji Frank
Mun ji labari cewa tsohon Mataimakin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC Timi Frank ya fito ya bayyana yadda Gwamnatin Najeriya ta so ta ci wa Atiku Abubakar mutunci daga dawowan sa Najeriya.

Asali: Original
Jaridar Vanguard ta rahoto yadda Timi Frank ya bankado sharrin da aka kitsawa ‘Dan takarar PDP na Shugaban kasa Atiku Abubakar a filin jirgi jiya bayan isowar sa Najeriya cikin tsakar dare daga hutun da ya tafi zuwa Garin Dubai.
Timi Frank wanda Jigo ne a Jam’iyyar APC kafin a fatattake sa daga Jam’iyyar ya fito da jawabi inda ya bayyana cewa Jami’an tsaro sun nemi sun tabbatar masu da cewa an aiko su ne domin su shiryawa ‘Dan takarar na PDP sharri.
KU KARANTA: 2019: Wani yaron Atiku ya caccaki Hadimar Shugaban kasa Buhari
Frank yace Jami’an da aka aiko sun bayyana masa cewa an turo su ne daga Fadar Shugaban kasa domin su tozarta Abokin takaran na Shugaba Buhari a zaben 2019. Jami’an sun laluba jirgin Atiku ko za su samu Daloli ba su samu ba.
Tsohon Mataimakin Sakataren yada labarai na kasa na Jam’iyyar APC yace Jami’an tsaron sun nemi su ajiye makudan kudi ca cikin jirgin saman na Alhaji Atiku Abubakar domin a samu dalilin yin ram da shi amma ba a kai ga yin nasara ba.
Frank a wata takarda da ya fitar da sa hannun sa ya nemi Kasashen waje su kawo masu doki inda ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta na yi wa Atiku da sauran manyan ‘Yan adawa barazana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng