Allah tsari kaka ta: Mustapha Atiku ya nuna cewa ba zai bi jirgin yakin Buhari a 2019 ba

Allah tsari kaka ta: Mustapha Atiku ya nuna cewa ba zai bi jirgin yakin Buhari a 2019 ba

– Wata Hadimar Buhari tace ‘Ya ‘yan su Atiku na iya komawa bayan Buhari

– ‘Daya daga cikin ‘Ya ‘yan ‘Atiku ya nuna cewa sam fa babu wannan labari

Allah tsari kaka ta: Mustapha Atiku ya nuna cewa ba zai bi jirgin yakin Buhari a 2019 ba
Onochie tace ‘Ya ‘yan cikin Atiku za su iya komawa bayan Buhari
Asali: UGC

Mun samu labari cewa daya daga cikin Hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafofin yada labarai watau Lauretta Onochie ta bayyana cewa kwanan nan irin su ‘Ya ‘yan Atiku Abubakar za su fito su goyi bayan tazarcen Buhari.

Lauretta Onochie tayi maganar nan ne bayan ta ji cewa Ditan Okupe wanda yana cikin ‘Ya ‘yan Doyin Okupe ya bayyana cewa zai marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zaben 2019. Dr. Okupe dai yana tare ne da Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Mutanen Madobi sun yi wa Kwankwaso kyakkyawar tarba a Kano

Onochie wanda ta ke aiki da Shugaba Buhari ta bayyana cewa sauran ‘Ya ‘yan Barayin kasar nan za su fito su marawa Buhari baya a zaben da za ayi a 2019. Onochie tace ba za tayi mamakin jin ‘Ya ‘yan Atiku sun fara kiran #SaiBuhari ba.

Mustapha Atiku Abubakar wanda yana cikin ‘Ya ‘yan ‘Dan takarar Shugaban kasar ya bayyana cewa duk wanda yake irin wannan tunani ya fado ta kai. Mustapha yace da alama Hadimar tana shaye-shaye da har ta ke irin wannan tunani.

A makon jiya ne dai wani tsohon Hadimin Shugaba Goodluck Jonathan Dr. Doyin Okupe ya rasa ‘Dan sa Ditan Okupe wanda ya bi Tawagan tazarcen Shugaba Buhari kamar yadda wani Yaron tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng