Shekau ya mayar da martani ga wadanda suka ce ya mutu (Bidiyo)

Shekau ya mayar da martani ga wadanda suka ce ya mutu (Bidiyo)

Shugaban kungiyar Jama'atu Ahlil Sunnah Lil Da'awatu Wal Jihad, da akafi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau ya saki sabuwar bidiyo inda ya ke jinjinawa mayakan kungiyar bisa nasarorin da suka samu a harin da suka kai a Kumshe, Gulumba da sauran sassan arewa maso gabashin Najeriya a baya-bayan nan.

Shekau ya bayyana a bidiyon sanye da khakin soji dauke da bindiga kirar AK 47 da kuma wasu masu gadinsa hudu a bayansa kuma yana cike da kuzari ba kamar yadda aka ganshi a bidiyon da ya saki a ranar 23 ga watan Yuli inda ya ke zaune a kasa ga kuma rashin kuzari.

Wannan karon Shekau ya tsaya da kafarsa har aka gama bidiyon mai tsawon mintuna bakwai da dakika 46 kamar yadda Sahara Reporters ta wallafa.

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Kamar yadda ya saba fadi, Shekau ya sake jadada cewa yana yaki da domin daukaka kalmar Allah da tabbatar da cewa musulunci ta yaddu a duniya har iya rayuwarsa.

"Ga wadanda suke cewa na mutu, su sani ba zan mutu ba har sai lokaci na ya yi," inji shi

Shugaban kungiyar ta Boko Haram kuma ya yi tsokaci kan hirar da kafar yadda labarai na VOA tayi da mahaifiyarsa a kwanakin baya.

Ga dai bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel