Gwamna El-Rufai ya sake nada mataimakiyarsa wani babban mukami a gwamnatin Kaduna

Gwamna El-Rufai ya sake nada mataimakiyarsa wani babban mukami a gwamnatin Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya sanar da kara ma Hajiya Dakta Hadiza Balarabe girma, inda ya nadata mukamin babban mashawarciya ga gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin gwamnan jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba a garin Kaduna, inda yace nadin mukamin ya fara yanzu yanzu.

KU KARANTA: Mutane 3 sun mutu, 5 sun yi batan bakatantan a wani hatsarin jirgin ruwa

Idan za’a tuna a satin daya gabata ne gwamnan jahar Kaduna ya sanar ya nada Hadiza mukamin mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna, wanda hakan ya janyo cece kuce a tsakanin al’ummmar jahar Kaduna.

Gwamna El-Rufai ya sake nada mataimakiyarsa wani babban mukami a gwamnatin Kaduna
Hadiza
Asali: UGC

Kafin wannan nadin da aka yi mata, Hajiya Hadiza ce shugaban hukumar kula da kananan asibitoci a matakan farko na jahar Kaduna, da wannan mukaminnata, Hajiya Hadiza za ta dinga sa idanu akan wasu manyan hukumomin gwamnati.

Daga cikin hukumomin da Hadiza Balarabe za ta dinga kulawa dasu akwai hukumar yan fansho ta jahar Kaduna, hukumar kula da taswirar jahar Kaduna KADGIS, da hukumar tsare tsaren birane ta jahar Kaduna, KASUPDA, tare da baiwa gwamna da mataimakinsa shawara.

“A matsayinta na babbar mashawarciyar gwamna, itace zuciyar gwamnatin jahar, da kuma halartar zaman majalisar tsaro da na zartarwa, haka zalika zata kasance guda daga cikin manyan jami’an gwamnatin jahar Kaduna a bayan gwmana da mataimakinsa.

“A kokarinsa na ganin dukkanin manyan jami’an gwamnatin jahar suna sane da halin da jahar take ciki, ire iren manyan jami’an nan sune manyan mashawartan gwamna, kuma sune masu zartar da dukkanin aikace aikace da manufofin gwamnatin.” Inji sanarwar.

Hadiza ce mace ta farko da ta fara shiga cikin wannan jerin manyan jami’an gwamnatin jahar Kaduna tun bayan tafiyar tsohuwar shugabar ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hadiza Bala Usman da ta koma hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel