Ana neman a kori ‘Daliban Kano da ke karatu a Sudan daga Makaranta saboda rashin kudi

Ana neman a kori ‘Daliban Kano da ke karatu a Sudan daga Makaranta saboda rashin kudi

Mun samu labari cewa wasu daga cikin ‘Daliban Jihar Kano da tsohon Gwamnan Jihar watau Rabiu Musa Kwankwaso ya tura karatu a 2014 a kasashen waje su faman fuskantar barazana a halin yanzu.

Ana neman a kori ‘Daliban Kano da ke karatu a Sudan daga Makaranta saboda rashin kudi

'Daliban da Kwankwaso ya tura Jami'ar Razi na iya dawowa gida
Source: UGC

Yanzu haka ana daf da fatattako ‘Daliban Jihar Kano da aka tura karatu a Jami’ar El-Razi da ke Kasar Sudan. Jami’ar ce dai ta aikowa Jihar Kano takarda inda ta sanar da ita cewa ana bin ta kudin Makarantar yaran ta da aka tura mata.

Wannan takarda da aikowa Gwamnatin Jihar tun a watan jiya ta shigo hannun me na kwanan nan. Shugaban Jami’ar da ke cikin babban Garin Khartoum a cikin Kasar Sudan watau Ahmad Rizq ne ya sa hannu a wannan gajerar wasika.

Hukumar Jami’ar ta sanar da Gwamnatin Jihar Kano cewa ‘Daliban ta da ke hannun ta ba su biya kudin makarantar wannan zango ba, inda aka kuma bayyana cewa za su iya fuskantar matsala wajen kammala karatun su a dalilin hakan.

KU KARANTA: Salihu Takai zai nemi Gwamnan Jihar Kano a zaben 2019

Yanzu dai har ta kai an haramtawa ‘Daliban na Jihar Kano da ke Jami’ar nan ta El-Razi shiga aji domin su dauki darasi. Idan dai aka kara mako guda ba a dauki wani mataki ba ‘Daliban za su gamu da cikas na karasa karatun da su ke yi.

A baya ne Rabiu Kwankwaso ya dauki wasu ‘Yan Kano ya aika su Jami’ar ta El-Razi wanda aka kafa shekaru kusan 17 da su ka wuce a Kasar Sudan domin su yi karatu da dukiyar Jiha. Sai dai yanzu Jihar ta gagara cigaba da biya masu.

A wancan lokaci tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa Gwamnati ta biya kaf kudin makarantar wannan Dalibai. Sai dai daga baya Gwamna mai-ci Abdullahi Umar Ganduje ya fara kukan an bar shi da bashin da ya fi karfin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel