Har yanzu Najeriya bata iya kama iskar gas da ta tono, tana zabga asara da lalata yanayi

Har yanzu Najeriya bata iya kama iskar gas da ta tono, tana zabga asara da lalata yanayi

- A cikin watanni biyar kacal Najeriya tayi asarar $416.224m

- Ya kamata gwamnati ta kawo karshen wannan lamari

- Kwamitin dake kula da bangaren gas tabbatar wa da yan Najeriya kawo karshen wannan lamari

Har yanzu Najeriya bata iya kama iskar gas da ta tono, tana zabga asara da lalata yanayi

Har yanzu Najeriya bata iya kama iskar gas da ta tono, tana zabga asara da lalata yanayi
Source: UGC

A cikin watanni Biyar Najeriya tayi asarar kudi $416.224m a sanadiyyar tsiyayewar Gas.

A wani bayani da NNPC ta fitar a watan Mayu 2018 kaso 10.64 na gas din da aka samar ya tsiyaye a cikin watanni biyar .

Sannan ta kara da cewa daga watan Jumairu zuwa watan Mayun shekara ta 2018 kasar ta siyar da Gas wanda adadin kudin yakai $608.73m da kuma $130.99,$ 101.05,$153,81,$ 161.18 da kuma $61.70m.

Kwamitin sanatoci a bangaren gas sun tabbatar wa da yan Najeriya kawo karshen tsiyayewar gas din kafin shekara mai zuwa.

DUBA WANNAN: 'Yan shia na kokarin zare ma soji ido da lasar takobi

Sanata Bassey Albert chairman na kwamitin ya bayyana haka ne a jihar Legas yayin wata ziyarar gani da ido da suka kai.

Ya kamata gwamnati ta kawo karshen wannan abu,amma kuma kamfononin mai sune suke dakatar da wannan abu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel