Sanata Shehu Sani ya hada fostar sa da ta Shugaban kasa Buhari
Mun samu labari cewa Sanatan nan na Kaduna ta tsakiya watau Shehu Sani yana neman taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe a 2019 duk da cewa Sanatan ya bar APC kwanakin baya.

Source: UGC
Sanata Shehu Sani ya fice daga Jam’iyyar APC kwanakin baya a dalilin rashin samun tikiti a Jam’iyyar mai mulki. Hakan ta sa Shehu Sani ya koma Jam’iyyar adawa ta PRP inda yake sa ran sake takarar Sanata a zaben 2019.
‘Dan Majalisar da yanzu yake neman tazarce ya gama fastocin sa da na Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Da alama duk da Sanatan ya sauya-sheka dai har yanzu yana tare da Shugaba Buhari wanda yake Jam’iyyar APC.
KU KARANTA: 'Yan kasuwa sun yiwa El-Rufai ihu, sunyi watsi da tayin da ya yi musu
Wannan abu dai ya ba jama’a mamaki ganin cewa Sanatan yana cikin masu sukar Shugaban kasar musaman bayan barin sa APC. ‘Dan Majalisar wanda yake wakiltar inda Shugaban kasa yake zama ya saba caccakar Gwamnatin sa.
A fastocin da su ke yawo yanzu a Kaduna, an ga hoton Sanata Shehu Sani wanda yake kokarin komawa Majalisar Dattawa tare da na wani Aminu S. Bello wanda yake neman kujerar Majalisar dokoki a karkashin PRP tare da hoton Buhari.
Sauran ‘Yan Jam’iyyar adawa ta PRP da-dama a Arewacin Kasar su na hada fastocin su da Shugaban kasa Buhari a zabe mai zuwa. A Jihar Kano ma dai akwai fastocin Sanata Isa Yahaya Zarewa da na Buhari su na yawo a Gari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng