‘Yan Shi’an Iran sun nemi Gwamnatin Najeriya ta fito da Zakzaky
Mun samu labari daga Jaridar The Cable cewa wasu Mabiya ‘Yan Shi’a da ke Kasar Iran sun nemi Gwamnatin Najeriya ta saki babban Malamin Shi’a da yake tsare watau Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Asali: Facebook
Wasu Kungiyoyin addinin Shi’a a Kasar Iran inda Mabiya Shi’a ke da karfi sun fara taso Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaba a dalilin garkame Jagoran Kungiyar IMN Malam Ibrahim Yakub El-Zakzaky.
Wani Bidiyo da ya shiga hannun Jaridar The Cable ya nuna yadda ‘Yan Shi’a da-dama a Kasar Iran su ke ihu su na kira ga Gwamnatin Tarayyar kasar ta fito da Ibrahim Zakzaky wanda yake daure tun karshen Disamban 2015.
KU KARANTA: Kasar waje sun fara tsoma baki kan rikicin Mabiya Shi’a da Jami’an tsaro
Masu zanga-zangar sun nuna cewa ko ba ji ma-ko ba dade dole sai an saki babban Malamin na Shi’a wata rana inda su kace za su kifar da Gwamnatin Najeriya su kuma saki shehin Malamin domin koyawa Najeriya darasi.
Yanzu dai kusan shekaru 3 kenan aka yi ana rufe da Ibrahim Zakzaky da Mai dakin sa a Najeriya duk da Kotu sun bada umarnin a fito da shi sannan kuma a gina masa gida tare da biyan sa makudan kudi na ci masa zarafi da aka yi.
‘Yan Shi’a dai su na cigaba da zanga-zanga har gobe a Najeriya tare da kira ga Gwamnati ta bi umarnin da Kotun kasar tayi, A ‘yan kwanakin nan ma dai an yi arangama tsakanin su da Jami’an tsaro a Garin Abuja.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng