An canza matsayin Akin Mustapha a Hukumar NDIC da Ronke Shokefun

An canza matsayin Akin Mustapha a Hukumar NDIC da Ronke Shokefun

Mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zare wani nadin mukami da yayi a Ma’aikatar NDIC ta kasa inda har ya aikawa Majalisar Tarayya wasika yana mai sanar da ita game da wannan mukami.

An canza matsayin Akin Mustapha a Hukumar NDIC da Ronke Shokefun
Shugaba Buhari ya maye gurbin Akin Mustapha a NDIC da wata mata
Asali: Depositphotos

Kamar yadda Jaridar The Cable ta rahoto cewa Shugaban kasa ya janye nadin mukamin da yayi wa Cif Olabode Akin Mustapha a matsayin Shugaban masu kula da Hukumar NDIC. Yanzu dai Shugaban kasar ya nada wata mata ne a mukamin.

Shugaban kasar ya fadawa Majalisar Dattawa ta takarda cewa ya nada Misis Ronke Shokefun ta maye gurbin da aka nemi a ba Akin Mustapha. Kawo yanzu dai dama Majalisa ba ta tabbatar da Cif Mustapha tun da aka aika mata sunan sa ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta karyata rade-radin canza wata Minista

Bayan wannan nadin kuma Shugaban kasar ya bada sunayen wadanda za su lura da Hukumar NBS mai tara alkaluman kasa. Kabiru Nakura ne aka zaba ya rinka kula da wannan Ma’aikata tare da wasu kwararrun mutane 5 da za su dafa masa.

Sauran wadanda za su rika sa-ido da abin da ake yi a Hukumar NBS ta kasar sun hada da Akinola Bashir, Moses Momoh, Walijo Danladi, Adamu Modu da kuma Nwafo Paul Chukwudi kamar yadda fadar Shugaban kasar ta sanar da Sanatoci.

Dazu kun ji Ministan yada labarai da al’adun Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana adana sama da Biliyan 17 a sanadiyyar rage facaka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng