An dawo da aikin jirgin kasa daga Kano zuwa Legas daga juma'ar nan
- Jiragen kasa daga Legas zuwa kano zasu dawo aiki a ranar juma'a
- An dakatar da amfani da jiragen ne sakamakon ruwan sama da ya wanke titin
- "Zamu koma aikin mu a ranar juma'a da izinin Ubangiji" inji Yakub

Asali: Depositphotos
Kamfanin jiragen kasa na Najeriya yace jirage daga Legas zuwa kano zasu koma aiki a ranar juma'a.
Mataimakin shugaban hulda da jama'a na kamfanin, Mr Mahmoud Yakub ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai a ranar litinin a garin Legas.
Yakub yace an tsaida kaiwa da kawowar jiragen kasan ne sakamakon ruwan sama da ya wanke titin jirgin.
"Zamu koma aiki a ranar juma'a, da izinin Ubangiji," inji shi
DUBA WANNAN: Anyi wa Tinubu kashedi kan Oshiomhole
Manajan jiragen kasa na yankin Legas, Mista Jerry Oche, yace an dakatar da kaiwa da kawowar jiragen ne saboda rafin Oyun na jihar Kwara da ya wanke titin jirgin.
"A yanzu da nake magana, jirgin kasan yana Ibadan kuma zai koma Kano a ranar juma'a. Mun kammala gyaran titin jirgin kuma jiragen zasu fara aiki a ranar juma'a in har baa fara yajin aikin ba," inji Oche
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng