'Yan bindiga a Katsina sun dauke diyar mutane bayan bindige ubanta
- Sun harbe shi ne da tsakar daren talata, ya cika a asibiti
- An kuma tabbatar sun tafi da diyarsa daga gidan
- A Kankiya abin ya faru

Asali: Twitter
Zargin cewa, gaggan 'yan fashin Zamfara sun fara tsiyaya jihar Katsina ya fara tabbbata, bayan da 'yan bindiga suka dirar wa wani hamshaki a daren jiya, suka halbe shi har lahira, suka kuma tafi da diyarsa maboyarsu.
Hukumar 'yansanda ta tabbatar da lamarin inda tace ana kan bincike, kan harin da barayi suka kai kan garin na Gachi, a karamar hukmar Kankia a katsinar.
Ana samun irin wadannan hare hare ne a jihar Zamara, amma da aka jibge jami'an tsaro, bayanan sirri sun nua sun tsere yazuwa jihohi makwabta.
DUBA WANNAN: Da muna da makamai da mun kashe soji - Shia
Tuni dai yau da safen nan, aka yi janazar Alhaji Nasiru Maimasara kamar yadda addininsa ya tanada, aka kuma shiga makoki, bayan da likitioci suka duba gawar tasa da sababin mutuwar tasa, abin tausayi.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng