Anyi addua'ar uku na Janar Alkali a fadar Sarkin Fika
A jiya ne akayi addua'ar uku na marigayi Manjo-Janar Mohammed Idris Alkali a fadar sarkin Fika da ke Potiskum a jihar Yobe.
Babban limamin masallacin garin Potiskum, Imam Mohammed Alkali Kalli ne ya jagoranci addu'an da aka gudanar misalin karfe 8 na safiyar yau inda dimbin al'umma da yan uwa da abokan arziki suka hallarta.
An yi addu'ar Allah ya gafartawa Alkali kurakurensa ya kuma saka masa da aljanna firdausi tare da sauran 'yan uwa musulmi da suka riga mu gidan gaskiya.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Sanatoci sunyi amai sun lashe a kan amincewa da bukatar Buhari
Shugaban kwamitin sarakunan Yobe, Sarkin Fika, Muhammadu Ibn Abali Muhammad Idrissa, jagoran iyalan marigayi Alkali, Air commodore Ibrahim Alkali, sauran masu rike da sarauta da mukamman gwamnati duk sun samu hallartan addu'an.
An dai gano gawar Janar Alkali ne a wata tsohuwar rijiya da ke jihar Plateau bayan hukumar soji da sauran jami'an tsaro sun kwashe kwanaki suna nemansa.
Hukumar Sojin tuni ta damke wasu mutane da ake zargi da hannu cikin kisan Alkali duk da cewa akwai wasun da har yanzu basu shigo hannu ba.
Baya ga Alkali, an kuma gano wata motar wani mutum da dan uwansa ya bayyana cewar ya bata tun shekarar 2013 bayan ya tafi jihar Plateau din don ya sayar da filinsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng