Jagaliya: An bawa hammata iska a kan rabon kyautar kudin da gwamnan APC ya bawa kungiya
Rikici ya kaure tare da doke-doke a tsakanin shugabanni da wasu fusatattun matasa da ke zargin jagororinsu sun ha'ince su a kan kyautar kudin shan ruwa, N300,000, da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya bawa gamayyar kungiyoyi fiye da 40 da su ka shirya taron gangamin nuna goyon bayan takararsa.
Kyautar kudi, N300,000, da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya bawa wata kungiya da ta kai ma sa ziyarar nuna goyon baya ga takarar sa ta haddasa fada da doke-doke tsakanin 'yan kungiyar.
Rikici ya kaure ne bayan gwamnan ya bukaci shugaban kungiyar, 'Congress Of Nigerian Eligible Voters (COEV)' ya dakata domin karbar kudin shan ruwa yayin da su ka kai masa ziyara a gidan gwamnatin jihar Jigawa da ke Dutse.
Mambobin kungiyoyin da su ka shirya taron gangamin nuna goyon baya ga takarar gwamna Badaru a karo na biyu, sun ziyarci gidan gwamnatin ne domin jaddada goyon bayansu da yin mubaya'a gare shi.

Asali: Depositphotos
Jagoran kungiyoyin da su ka shirya taron gangamin, John Offia, ya shaidawa manema labarai cewar su na goyon bayan takarar gwamna Badaru ne saboda irin aiyukan raya kasa da ya shimfida a kananan hukumomin jihar Jigawa.
Daga cikin aiyukan da Offia ya lissafa akwai inganta asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a kauyuka, gina sabbin asibitoci da kuma kara kasafin bangaren lafiya domin inganta lafiyar mutanen jihar Jigawa.
A nasa jawabin, gwamna Badaru ya godewa kungiyar bisa yaba ma sa a an aiyukan da ya yi duk da kasancewar ya fuskanci matsalar karancin kudade a kwanakin farko na hawansa kujerar gwamna.
DUBA WANNAN: Wargatsewar Kwankwasiyya: Farfesa Hafizu ya fito takarar gwamna a PRP ta Aminu Kano
Bayan kammala taron ne sai gwamna Badaru ya damka N300,000 da Mista Offia domin shu sha ruwa amma sai rikici ya barke bisa zargin cewar gwamnan ya ba shi adadin kudin da ya gabatar ga ragowar mutanen da su ka yi taron gangamin tare.
Fusatattun 'yan kungiyar sun nuna shakku tare da bayyana cewar babu yadda za a yi gwamnan ya bayar da N300,000 kacal ga taron kungiyoyi fiye da 40.
Da kyar jami'an 'yan sanda su ka kwaci Ibrahim Kwaciri, daya daga cikin shugabannin taron da fusatattun matasa su ka rike.
Wata shugabar mata, Hajiya Fati, ta koka bisa yadda aka ba ta N3,000 domin rabawa ga mata fiye da 50 da ta kawo daga wurare daban-daban domin halartar taron gangamin. Kazalika ta zargi shugabannin taron da ha'intar su tare da bayyana cewar ba zasu dauki maganar da wasa ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng