Mutane su na zuzuta karfin Tinubu a siyasar Kasar nan – Inji Oby Ezekewsili

Mutane su na zuzuta karfin Tinubu a siyasar Kasar nan – Inji Oby Ezekewsili

Mun samu labari cewa daya daga cikin ‘Yan takarar Shugaban kasa a zaben 2019 Dr Oby Ezekwesili ta bayyana cewa jama’a su na zuzuta karfin babban Jigon nan na Jam’iyyar APC watau Bola Tinubu.

Mutane su na zuzuta karfin Tinubu a siyasar Kasar nan – Inji Oby Ezekewsili
Dr. Oby Ezekewsili tace mutanen Najeriya ne su ka kyale su Tinubu su ke mulkar su
Asali: Depositphotos

Madam Oby Ezekwesili ta nuna cewa za ta lashe zabe mai zuwa duk da ba ta da wani tsari kafe a kasa kamar yadda sauran manyan Jam’iyyu irin su APC su ke da shi. ‘Yar takarar tace mutane su na zuzuta karfin kafuwar Jam’iyyun kasar.

A jawabin na tsohuwar Ministar, ta bayyana tasirin Bola Tinubu bai kai yadda mutane su ke nunawa ba domin kuwa duk da karfin sa da ake ta yayatawa a siyasa, kuri’u kadan Jam'iyyar sa ta APC ta samu a Garin Alimosho a zaben ya wuce.

KU KARANTA: Atiku yayi wani zama a boye da su Saraki da Peter Obi a kasar Larabawa

Ezekwesili ta ke cewa duk da akwai sama da kuri’u 650, 000 a Garin Alimosho mai mutum fiye da Miliyan 1.2, sai dai a lokacin zabe mutane 140, 000 ne rak ne su ka fito su ka kada kuri’ar su inda mutane 86, 897 ne kacal su ka zabi APC.

Mai neman shugaban kasar a ACPN ta nuna cewa an kyale su Asiwaju Bola Tinubu ne su na cin karen su babu babbaka amma tace dole a taka masu burki a halin yanzu. Ezekwesili tace abin da kamar wuya amma za ta iya lashe zaben 2019.

Kwanaki dai kun ji cewa Oby Ezekwesili, tayi kaca-kaca da Atiku Abubakar kan alkarin sa na rage kudin man fetur. 'Yar takarar tace shakka babu Atiku bai fahimci komai a kan tattalin arzikin Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: