'Yan daba sun gwabza da fusatattun masoya Atiku

'Yan daba sun gwabza da fusatattun masoya Atiku

Wasu 'yan daba sun tarwatsa taron manema labarai da wasu fusattatun magoya bayan dan takarar shugabancin kasa, Atiku Abubakar karkashin kungiyar Aggirieved Atiku Support Groups (AASG) suka shirya a ranar Litinin a Abuja.

'Yan kungiyar AASG din sunyi imanin wasu da ba su kaunar ganin sun shiga ofishin yakin neman zaben Atiku ne suka turo 'yan daban su tartwatsa taronsu.

'Yan daban sunyi nasarar kwace fostoci da fusattatun magoya bayan Atikun ke dauke da shi kuma suka tsere da shi.

Ciyaman din AASG, Osaratin Godspower ya shaidawa manema labarai cewar sun kira taron manema labaran ne domin su sanar da duniya abubuwan da ke faruwa a kungiyar yakin neman zaben Atiku.

'Yan daba sunyi arangama da magoya bayan Atiku
'Yan daba sunyi arangama da magoya bayan Atiku
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Fallasa: An gano yadda gwamnatin Buhari ta waske da N378bn

A yayin da ya ke nuna rashin jin dadinsa, Godspower ya ce abin takaici ne yadda yanzu ake Kungiyar yakin neman zaben Atiku (APCO) ke kiransu 'yan bayar da gudunmawa' inda ya ce ba zai yiwa wasu su rika aiki ba amma wasu na karbar kudade.

Godspower ya ce cin mutunci ne ya sa wasu ke kiransu masu bayar da gudunmawa duk da cewar sun yiwa Atiku ayyuka daban-daban cikinsu har da wadanda suka hada kudi domin siyawa Atiku tikitin takarar shugabancin kasa.

Ya kara da cewa muddin ba a dauki mataki kan wannan lamarin ba, Atiku yana iya rasa kuri'u a babban zaben 2019 mai zuwa. Ya ce suna son a daraja su a matsayin wadanda suka yiwa Atiku aiki.

Daga karshe AASG ta bukaci a shirya taro na musamman inda za su gana da Atiku Abubakar domin a magance matsalar ta yadda za a rika damawa da su cikin kungiyar yakin neman zaben na Atiku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164