Wargatsewar Kwankwasiyya: Farfesa Hafizu ya fito takarar gwamna a PRP ta Aminu Kano

Wargatsewar Kwankwasiyya: Farfesa Hafizu ya fito takarar gwamna a PRP ta Aminu Kano

- Yanzu haka dai jam'iyyar PRP na cigaba da karbar manyan 'yan siyasa daga APC da PDP a jihar Kano

- Tun kafin Farfesa Hafizu ya shiga PRP, tsohon kwamishina kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Mallam Salihu Sagir Takai, ya koma jam'iyyar ta PRP

- Da ya ke jawabi yayin ziyarar da ya kai ofishin jam'iyyar, Farfesa Hafizu, ya bayyana cewar ya shiga PRP din ne saboda kyawawan manufofinta

Farfesa Hafizu Abubakar, tsohon mataimakin gwamnan Kano da ya yi murabus, ya ziyarci ofishin jam'iyyar PRP bisa rakiyar dumbin magoya bayansa domin nuna sha'awar sa ta yin takarar gwamna a inuwar jam'iyyar.

A cikin satin da ya gabata ne Farfesa Hafizu ya canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar PRP bayan ya zargi PDP da rashin karrama shi duk da kasancewar ya yi murabus daga mukaminsa domin komawa cikinta.

Farfesa Hafizu ya ajiye mukaminsa na mataimakin gwamnan jihar Kano tare da komawa jam'iyyar PDP, tsagin Kwankwasiyya, da niyyar samun tikitin takarar gwamna.

Wargatsewar Kwankwasiyya: Farfesa Hafizu ya fito takarar gwamna a PRP ta Aminu Kano
Farfesa Hafizu Abubakar
Asali: Depositphotos

Tun kafin Farfesa Hafizu ya shiga PRP, tsohon kwamishina kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Mallam Salihu Sagir Takai, ya koma jam'iyyar ta PRP domin yin takarar gwamna bayan takarar da ya ke yi a PDP ta samu cikas.

DUBA WANNAN: Bidiyon cin hanci: Akwai bukatar Buhari ya gaggauta bincikar Ganduje - SERAP

Yanzu haka dai jam'iyyar PRP na cigaba da karbar manyan 'yan siyasa daga APC da PDP.

Da ya ke jawabi yayin ziyarar da ya kai ofishin jam'iyyar, Farfesa Hafizu, ya bayyana cewar ya shiga PRP din ne saboda kyawawan manufofinta da ya sani tun a shekarar 1978, lokacin yana dalibi.

Sannan ya kara da cewar bai ga jam'iyya, a halin yanzu, da ke da kyawawan manufofi kamar na PRP ba.

Yanzu dai ana zaman jiran ganin yadda jam'iyyar ta PRP za ta yi da 'yan takarar ta na kujerar gwamna, musamman ganin cewar lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)) taiba domin yin zabukan fidda 'yan takara ya wuce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng