An taso Atiku Abubakar a gaba na yin taron siyasa a Birnin Dubai
Wata Kungiya mai suna “New Agenda for Positive Change” ta caccaki ‘Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa watau Atiku Abubakar game da shirin da yake yi game da zaben.

Asali: UGC
Kungiyar tayi tir da taron da Atiku Abubakar ya shirya tare da sama da mutane 400 a Birnin Dubai da ke cikin Kasar UAE. Atiku dai ya tare a Dubai ne da mutanen sa inda yake cigaba da shiryawa yadda za a bullowa zaben 2019 da kyau.
Daga cikin wadanda su ka halarci wannan taro akwai Abokin takarar sa watau Peter Obi da kuma tsohon Darektan yakin neman zaben sa Gbenga Daniel da kuma Reno Omokri wanda ya taba aiki da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
KU KARANTA: 2019: Mataimakin Atiku ya kai wa Kwankwaso ziyara har gida an sa labule
Sauran wadanda su ka halarci wadannan taro sun hada da Bukola Saraki wanda yanzu haka shi ne Sarkin yakin neman zaben Atiku a 2019 da kuma Sanata Ben Murray Bruce. Kungiyar tace wannan ya nuna cewa Atiku mabarnacin gaske ne.
Shugaban wannan Kungiya watau Raymond Clarke Amuna ya bayyana cewa wannan shiri da Atiku yake yi a Kasar UAE ya nuna cewa Najeriya za ta karkatar da hankalin ta ne zuwa ga kasashen waje idan Atiku ya samu mulkin kasar nan.
Wannan Kungiya da ke kokarin ganin an kawo canji a Kasar ta kuma bayyana cewa mutumin da yake taro da ‘Yan siyasa barkatai a kasar waje ba zai iya rike Najeriya idan ya samu dama ba domin kuwa ko da yayi mulki facaka aka rika yi a kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng