Kisan Janar Idris Alkali: Hoton mutane 19 da hukumar 'yan sanda ta yi bajakolinsu

Kisan Janar Idris Alkali: Hoton mutane 19 da hukumar 'yan sanda ta yi bajakolinsu

- A yau, Lahadi, ne hukumar 'yan sanda reshen jihar Filato ta yi bajakolin wasu mutane 19 da ke da nasaba da kisan Janar Idris Alkali

- Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta rawaito cewar an bayyana batan janar Alkali ne a ranar 3 ga watan Satumba bayan ya bar Abuja zuwa Bauchi

- A ranar 31 ga watan Oktoba ne aka gano gawar Janar Alkali a wata tsohuwar rijiya da yankin Gushwet a unguwar Shen a karamar hukumar Jos ta kudu

A yau, Lahadi, ne hukumar 'yan sanda reshen jihar Filato ta yi bajakolin wasu mutane 19 da ke da nasaba da kisan Janar Idris Alkali a garin Jos.

A yau ne kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, Terna Tyopev, ya yi bajakolin mutanen ga manema labarai a garin Jos.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta rawaito cewar an bayyana batan janar Alkali ne a ranar 3 ga watan Satumba bayan ya bar Abuja zuwa Bauchi.

Kisan Janar Idris Alkali: Hoton mutane 19 da hukumar 'yan sanda ta yi bajakolinsu
Hoton mutane 19 da hukumar 'yan sanda ta yi bajakolinsu
Asali: Twitter

A ranar 29 ga watan na Satumba ne aka samu motar janar Alkali a wani kududdufi mai zurfin gaske da ke yanki Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu.

A ranar 31 ga watan Oktoba ne aka gano gawar Janar Alkali a wata tsohuwar rijiya da yankin Gushwet a unguwar Shen a karamar hukumar Jos ta kudu. Hukumar soji ta binne gawar Marigayi Alkali a jiya, Asabar, 3 ga watan Nuwamba.

DUBA WANNAN: Tsige Oshiomhole: Gwamnonin APC sun fara neman hadin kan sanatocin da basu ci zabe ba

A cewar Tyopev, mutanen 19 sun hada da mutane 13 da hukumar soji ta kama kuma ta damka hannun jami'an 'yan sanda, yayin da ragowar 6 na daga cikin mutane 8 da hukumar ta sanda ta bayyana nemansu ruwa a jallo.

Kakakin ya kara da cewar, har yanzu rundunar 'yan sanda na cigaba da neman mutane biyu daga cikin wadanda ake zargi da kisan marigayi Alkali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng