2019: Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari, hotuna

2019: Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari, hotuna

Shugabannin kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo, karkashin jagorancin tsohon suhgaban majalisar dattijai, Sanata Ken Nmani, sun ziyarci shugaba Buhari a fadar sa, yau, Asabar, 03 ga watan Nuwamba, 2018.

Yayin da ya ke yaba ma su bisa ziyarar da su ka kai ma sa, shugaba Buhari ya taya Nmani murnar cika shekara 70 a duniya tare da yabawa irin gudunmawar da ya bayar wajen tafiyar da gwamnati da taimakawa wajen dorewar mulkin dimokradiyya a Najeriya.

Wasu rahotanni na nuna cewar ziyarar kungiyar 'yan kasuwar na da fuska ta siyasa, har wasu ma su fashin alkaluma na kari da cewar shugaba Buhari zai samu goyon bayan shugabannin yankin a zaben shekarar 2019.

2019: Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari, hotuna
Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari
Source: Twitter

2019: Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari, hotuna
Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari
Source: Twitter

2019: Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari, hotuna
Kungiyar 'yan kasuwar kabilar Igbo sun ziyarci Buhari
Source: Twitter

A wani labarin sabanin wannan, kun ji cewar a daidai lokacin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa kuma 'yan siyasa ke neman goyon jama'a, matasan yankin kudu maso yamma na 'yan kabilar Yoruba sun yi fatali da tayin Atiku na bawa yankinsu kujerar sakataren gwamnatin tarayya (SGF) idan ya zama shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Ka zo mu baka nasara a zaben 2019 - Guru Maharaji ya fadawab Buhari

Kazalika matasan sun ce jam'iyyar PDP ba ta taba cika alkawarin da ta daukar wa yankin ba a baya.

Matasan karkashin kungiyar 'Yoruba Youth Congress' ta zargi jam'iyyar PDP da yiwa yankinsu kallon ta fuskar rabon mukaman gwamnati lokacin da ta ke kan mulki.

Shugaban kungiyar, Mista Kola Salawu, ya shaidawa 'yan jarida cewar jam'iyyar APC ce ya share hawayen jama'ar yankin ta hanyar ba su kujerar mataimakin shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng