Sabo: An haramtawa Asia Bibi barin Pakistan bayan zama shekaru 10 a kurkuku, duk da tana cikin hadari
- Pakistan ta kawo karshen zanga zanga da akeyi akan Asia Bibi
- An daure Asia ne tun a shekara ta 2010
- Gwamnati bazata iya kare masu zanga zanga akan hukuncin da kotu tayi ba

Asali: UGC
Wasu kungiyoyi a Pakistan sun nuna rashin amincewar su akan hukuncin da akayiwa wata mata kirista mai suna Asia Bibi wadda tayi wasu kalamai na tozarci ga Annabin Musulmi Muhammad.

Asali: Twitter
Gwamnati ba zata iya kare mutanen da suka fito suna bore akan hukuncin na cewa Asia zatabar kasar ba.
Haka kuma idan jama'a suka tashi kasheta, da kyar in za'a iya kawar dasu a kare ta.
DUBA WANNAN: Shekaru nawa Ganduje zayyi a kulle?
An kamata ne a shekara ta 2010 amma an wanke ta tas ta a cikin wannan satin, bisa dalilan rashin cikakkiyar hujja.

Asali: Facebook
Minista watsa labarai na Pakistan Fawad Chaudhry ya bayyana BBC cewa "zabi biyu garesu ko su sanya karfi wanda hakan zai iya janyo kashe kashe, gwamnati kuma bazata so faruwar haka ba, ko kuma su bi doka da oda su girmama dan-adam"
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng