EFCC Ta Kama Sunan Masu Hantararta kan Shari'ar Tsohon Gwamna a Najeriya

EFCC Ta Kama Sunan Masu Hantararta kan Shari'ar Tsohon Gwamna a Najeriya

  • EFCC ta ce tana fuskantar matsin lamba daga ’yan Najeriya saboda jinkirin kammala wasu manyan shari’o’in rashawa da take gudanarwa a kotuna
  • Hukumar ta ambaci shari’ar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, a matsayin ɗaya daga cikin shari’o’in da suka jawo mata suka
  • EFCC ta ce ba ita ce ke da ikon yanke hukunci ba, domin aikinta shi ne bincike da gurfanar da waɗanda ake zargi, yayin da kotuna ke yanke hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta ce tana fuskantar matsin lamba da suka daga jama’a saboda rashin kammala wasu manyan shari’o’in da take gudanarwa a kotuna daban-daban.

Hukumar EFCC ta ambaci shari’o’in zargin almundahana da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin wasu daga cikin shari’o’in da suka jawo mata fushin ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake ta'addanci, an kashe mutane da sace bayin Allah a Kaduna

EFCC ta yi magana kan Yahaya Bello
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello Hoto: EFCC Nigeria, Alhaji Yahaya Bello
Source: Twitter

Daily Trust ta ce mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani taron haɗin gwiwa na masu magana da yawun hukumomin tsaro, ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026.

EFCC ta nemi jama’a su fahimci tsarin shari’a

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa wasu shari’o’i ke kammaluwa cikin sauri, yayin da wasu ke ɗaukar shekaru, Oyewale ya buƙaci ’yan Najeriya su fahimci yadda tsarin shari’a yake aiki.

Ya ce EFCC ba kotu ba ce, don haka ba za ta iya zama mai tuhuma da kuma alƙali a kan shari’ar da kanta ta shigar ba.

A cewarsa, dokokin da suka kafa hukumar sun ba ta ikon gudanar da bincike, gurfanar da waɗanda ake zargi da kuma hana aikata laifufdukan cin hanci da rashawa.

Sai dai ya jaddada cewa ba ta da ikon sauraron shari’a ko yanke hukunci kan waɗanda ta gurfanar.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado haramtacciyar matatar mai ta 'yan kasar waje cikin daji

"Ina ganin yana da muhimmanci a wannan taro mu fahimci matakai da tsarin da ake bi wajen gurfanar da mutane a gaban kotu. EFCC a matsayinta na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ba ita ce ɓangaren shari’a ba.

“Ba za mu iya zama masu tuhuma da kuma alƙalai a kan shari’ar da kanmu muka shigar ba.” In ji shi.

Hukumar ta ce kotu ce ke da ikon yanke hukunci

Mai magana da yawun hukumar ya bayyana cewa ba za a iya kai ƙara kotu sannan a tilasta wa alƙalai su kammala ta cikin kwana biyu ko uku ba.

Ya ce alhakin yanke lokacin da za a kammala shari’a yana hannun bangaren shari’a, yayin da EFCC ke gabatar da hujjojinta kamar yadda sauran ɓangarorin shari’a suke yi.

Ya ƙara da cewa idan shari’a ta kammala cikin sauri, hukumar za ta yaba wa kotu, amma idan aka samu jinkiri saboda wasu matsaloli, bai kamata a ɗora wa EFCC laifi ba.

“Idan aka gurfanar da mutum a kotu, sai ku ce EFCC za ta yanke lokacin da za a kammala shari’ar. A’a, ba mu da irin wannan iko.” In ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna bayan yi wa 'yan sanda kwanton bauna a Zamfara

EFCC ta yi magana kan shari’ar Yahaya Bello

Hukumar ta bayyana cewa tana fuskantar yawan tambayoyi da matsin lamba daga jama’a musamman kan shari’ar Yahaya Bello, wanda ake tuhuma da wasu laifuffukan da suka shafi rashawa.

Oyewale ya ce EFCC ta riga ta shigar da shari’ar gaban kotu, kuma ana sauraron wasu ɓangarorinta a kotuna biyu daban-daban.

Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su taimaka wajen wayar da kan jama’a game da rawar da kowace hukuma ke takawa a tsarin shari’a.

Kakakin ya kuma bayyana cewa shari’ar tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, wadda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari, ta kammala cikin sauri saboda wasu matakai da aka bi a kotu.

Sai dai ya ce wasu shari’o’in kan kasance masu sarkakiya saboda yawan shaidu da sauran batutuwan da ke buƙatar kulawa kafin a yanke hukunci.

EFCC ta yi magana kan shari'ar Yahaya Bello
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto': @OfficialEFCC
Source: Facebook

EFCC ta bankado matatar mai a daji

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta ce ta gano wata matatar mai da ake gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ogere, Jihar Ogun, wadda ake zargin wasu ’yan China ne ke sarrafawa.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa jami’anta sun gano matatar ne a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, bayan tattara bayanan sirri da kuma sa ido kan ayyukan mutanen da ke tace dattin mai ba bisa ƙa’ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng