Siyasar Kano: Shekarun da Ganduje zayyi a kurkuku muddin aka same shi da laifi

Siyasar Kano: Shekarun da Ganduje zayyi a kurkuku muddin aka same shi da laifi

- Wani lauya yace idan aka tabbatar da zargin da akeyiwa Ganduje zai shafe shekaru 171 a gidan yari

- An turo wasu bidiyo ne dake nuni na gwamnan a lokacin da yake karbar nagoro.

- Jaridar Daily Nigerian tace tana da wasu fefan bidiyo guda 9 da yake nuna da gwamnan yana karbar nagoro a mababbantan lokuta

Siyasar Kano: Shekarun da Ganduje zayyi a kurkuku muddin aka same shi da laifi
Siyasar Kano: Shekarun da Ganduje zayyi a kurkuku muddin aka same shi da laifi
Asali: Twitter

Wani lauya dan kasar Najeriya Audu Bukarti yace matukar aka tabbatar da zargin da ake yiwa gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje to fa zai share shekaru 171 a gidan Kaso.

Bayan zaman gidan kaso gwamnan zai biya tarar Dala miliyan $30.

"Kamar yanda muke cigaba da kallon wadannan bidiyo dake nuni da gwamnan yake karbar na goro wanda yakai dala miliyan $5, ina bayyana irin kalubalen dazai fuskanta idan aka kamashi da laifin.ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

DUBA WANNAN: An ceto yaro daga hannun matsafa

"Hukumar EFCC, Penal code da kuma ICPC zasuyi bincike akan Ganduje sannan kowacce hukuma da nata hukuncin".

Sannan kuma zai dawo da kudin daya karba kuma biyan bazai haure sau biyar ba. Gwamna Ganduje na fuskantar kalubale kuma zai iya rasa kujerarsa kain zaben 2019, shi Kuwa Gawuna, shi ne zai sami kujerar a fala.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng