Karanta wasu muhimman bayanai 10 game da Hadiza sabuwar mataimakiyar Gwamna El-Rufai

Karanta wasu muhimman bayanai 10 game da Hadiza sabuwar mataimakiyar Gwamna El-Rufai

A ranar Juma’a 2 ga watan Nuwamba ne gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da sunan Hajiya Hadiza Balarabe a matsayin sabuwar mataimakiyarsa, da za ta maye gurbin Barnabas Bala Bantex, wanda zai tafi neman mukamin Sanata.

A cikin wata hira da El-Rufai ya yi da manema labaru a kwanakin baya ne ya bayyana ma Duniya cewa mataimakinsa, Bala Bantex zai nemi takarar Sanatan mazaba ta uku a jahar Kaduna, wato kudancin Kaduna ne kenan, don haka a cewarsa yana ta bincike domin lalubo sabon mataimaki.

KU KARANTA: Shari’a sabanin hankali: Kotu ta fatattaki wani dan majalisa, ta nemi ya dawo da albashin da ya ci

Karanta wasu muhimman bayanai 10 game da Hadiza sabuwar mataimakiyar Gwamna El-Rufai
Hadiza da Gwamna El-Rufai
Asali: Twitter

Sai ga kwatsam a yau Juma’a, kaakakin gwamnatin jahar, Samuel Aruwan ya bada sanarwar cewa a bincike da Gwamna El-Rufai ya yi, ya gano babu wani mahalukin da yafi cancanta da wannan mukami kamar Hajiya Hadiza Balarabe, don haka Legit.com ta hako wasu bayanai game da ita kamar haka;

- A shekarar 1966 aka haifi Hadiza Balarabe

- Hadiza yar kabilar Gwantu ce daga karamar hukumar Sanga

- Ta kammala karatun Likitanci a shekarar 1988 daga jami’ar Maiduguri

- Babbar likitace a jami’ar Ahmadu Bello

- Ta rike mukamin Daraktan kiwon lafiya a babban birnin tarayya Abuja a shekarar 2004

- Ta rike mukamin shugaban hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko

- Itace mace ta farko Musulma da ta fara zama mataimakiyar gwamna a Kaduna

- itace mace ta biyu da ta taba zama mataimakiyar gwamna a Kaduna

- A yanzu haka tana kasar Kenya aka nadata mukamin mataimakiyar gwamnan Kaduna

Sai dai masana siyasar jahar Kaduna suna ganin akwai babban kalubale ga gwamnan musamman ga bukatarsa ta zarcewa akan mukaminsa, tunda a tarihin jahar Kaduna daga 1999 ba’a taba yin gwamna musulmi, mataimaki musulmi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng