Dalilin da ya sanya nake jin takaicin Majalisar Tarayya - Shugaba Buhari

Dalilin da ya sanya nake jin takaicin Majalisar Tarayya - Shugaba Buhari

A yau Juma'a cikin babban birnin kasar nan na tarayya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilansa dangane da yadda al'amurran Majalisar dokoki ta tarayya ke matukar ci ma sa tuwa a kwarya tare da kuntatawa gami da bacin rai.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana bacin ran sa gami da kunci dangane da yadda 'yan majalisar dokoki ta tarayyar kasar nan ke kawo tsaiko da nawa a duk sa'ilin shigar da duk wani kudiri na kasafin kudi cikin dokar kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, wannan tafiyar hawainiya gami da jan gindi da majalisar tarayya ke aiwatar yayin bayar da sahalewarta kan kudirirrikan kasafin kudi na kawo tsaiko da nawa ta kammala wasu muhimman ayyuka a kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin wasu manyan baki daga jihar Neja, wanda tsohon babban Sojin kasa, Janar Garba Buba ya jagorancin tawagarsu zuwa fadar Villa dake garin Abuja.

Dalilin da ya sanya nake jin takaicin Majalisar Tarayya - Shugaba Buhari
Dalilin da ya sanya nake jin takaicin Majalisar Tarayya - Shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

A sanadiyar haka shugaba Buhari yake fata gami da sa ran majalisar tarayya za ta sauya wannan taku domin tabbatar da gwamnatin tarayya ta kammala kudirirrika na muhimman ayyuka da ta nufaci kammalawa.

KARANTA KUMA: Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan Mutane 13 a jihar Borno

Kazalika shugaba ya shaidawa tawagar manyan bakin da ta hadar har da tsohon gwamnan jihar Neja na lokacin mulkin soji, Abubakar Bello cewa, gwamnatin sa za ta kara kaimi tare da bayar da muhimmancin gaske wajen shimfida manyan hanyoyi na tituna a fadin jihar da kuma kasa baki daya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar jarrabawar kammala makarantar Sakandire ta WAEC, ta bayyana takardar shaidar shugaba kasa Buhari da a baya ake faman huro ma sa wuta ya gaza gabatar da ita.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng