Kasar Israila na kashedi kan yiwuwar barkewar rikici a Najeriya gabanin zaben 2019
- Ofishin jakadancin Isra'ila dake Najeriya ta ja kunnen 'yan Nageriya akan tada tozarma a wajen zabe
- A duk lokacin da ake kokarin gina wani abu to dole ne ka fuskanci kalubale
- An nemi Nageriya data dauke Jakadancin ta zuwa Jerusalem

Asali: Twitter
Ofishin jakadancin Isra'ila dake Najeriya yayi kira ga 'yan kasar nan da su guji tada tarzoma a lokacin zabe.
Ofishin yayi wannan kira ne a jiya a wajen bikin tunawa da cika shekaru 23 da rasuwar Shugaban kasar ta Isra'ila Yitzhak Rabin.
Bisa ga gabatowar zaben shekara ta 2019 za'ayi ta ganin abubuwa na rikici kala kala, jakadan Yahudun, Mr Nadev Goran yace yana baiwa 'yan siyasa shawara da suyi koyi da marigayi tsohon shugaban kasar su.
DUBA WANNAN: Tsakani da Allah nake aiki na - Prof. Usman
Ya kara da cewa aduk lokacin da kake kokarin gina kasa zaka fuskanci kalubale iri iri wanda yake janyowa jikin mutum yai sanyi wanda kadan ne suke samu su haura zuwa wannan matsayi.
Sannan muna kira ga gwamnatin Nageriya data dauke jakadancin ta daga Tel Aviv zuwa Jerusalem Wanda shine burin yan Nageriya da dama.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng