Masu Garkuwa da Kansiloli 2 na jihar Katsina sun bukaci fansa ta N50m

Masu Garkuwa da Kansiloli 2 na jihar Katsina sun bukaci fansa ta N50m

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito za ku ji cewa, wadanda ke garkuwa da Kansiloli biyu na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, sun nemi fansar makudan dukiya ta wuri mai gugar wuri har Naira Miliyan hamsin.

A ranar Larabar da ta gabata ne masu garkuwa da Mutane suka yi awon gaba da Hussani Wanzam da kuma Bashin Dan Jikko yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida a karamar hukumar Batsari bayan sun kammala aikace-aikacen su kamar yadda suka saba.

Wata sahihiyar majiya da ta zayyanawa manema labarai wannan rahoto ta bayyana cewa, masu garkuwar sun bukaci fansar makudan dukiya da ta kai Naira miliyan Hamsin.

Masu Garkuwa da Kansilolin jihar Katsina sun bukaci fansa ta N50m
Masu Garkuwa da Kansilolin jihar Katsina sun bukaci fansa ta N50m
Asali: Twitter

Kazalika hukumar 'yan sanda ta jihar ta bayar da tabbacin tsayuwar dakanta wajen ceto wannan manyan 'yan siyasa biyu yayin da ta ke matsanta sintiri da kai komo wajen gudanar da bincike na diddigi.

KARANTA KUMA: Mutane 97 sun gurfana gaban Kuliya kan rikicin jihar Kaduna

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiyar Alhamis tsautsayi na garkuwa ya afka kan wasu ma'aikatan lafiya uku a babbar hanyar garin Toto dake jihar Nasarawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng