Sakataren yadda labaran PDP a arewa ya fice daga jam'iyyar
Sakataren yadda labarai na arewa maso yamma na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Yusuf Babura, ya yi murabus daga matsayinsa.
A yau, Alhamis 1 ga watan Nuwamba, Babura ya shaida wa kamfanin dillancin labarai (NAN) a Dutse cewar ya fice daga jam'iyyar PDP.
Ya yi bayyanin cewar babu wanda ya tilasta masa yin murabus din kuma a halin yanzu yana tattaunawa da magoya bayansa kan jami'iyyar ta zai koma.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Kudin makamai: Kotu ta yi babbar barazana ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP
Babura ya mika godiyarsa da mabobin tsohuwar jam'iyyarsa saboda irin gudunmawar da suka bashi lokacin da ya yi aiki tare da su.
"Ina rokon dukkan wadanda na yiwa laifi da, wanda na sani da wanda ban sabi ba suyi min afuwa," inji shi.
A wata rahoto mai kama da wannan, Legit.ng Hausa ta kawo muku cewar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP. Hafiz ya ce zai bayyana jam'iyyar da zai koma nan da kankanin lokaci.
Da aka tuntube shi domin samun tabbas kan labarin ficewarsa daga jam'iyyar ta PDP, Hafiz ya ce, "Da gaske ne na fice daga PDP, zanyi jawabi nan ba da dadewa ba,"
Wasikar murabus dinsa daga PDP yana da yawo a kafafen yada labarai da sada zumunta cikin kwanakin nan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng