Idan Atiku ya samu mulki zai gina kan sa ne da dukiyar Najeriya - Oby Ezekwesili
Mun samu labari cewa tsohuwar Ministar ilmi da kuma ma’adanai ta Najeriya Oby Ezekwesili wanda tana cikin masu neman takarar Shugaban kasa a zaben 2019 ta fara kokarin ta tona asirin Atiku Abubakar.

Asali: Twitter
Madam Oby Ezekwesili ta fara bankadowa Duniya sirrin Atiku Abubakar game da sha’anin kasuwancin sa. Ezekwesili tace maganar Atiku zai habaka tattalin arziki idan ya samu mulki saboda ya kware a harkar kasuwanci sam ba gaskiya bane.
Tsohuwar Ministar tace jama’a da-dama ba su taba samun labarin abin da Kasar Amurka ta fada game da Jami’ar da Atiku Abubakar ya gina a lokacin yana mulki ba. Ezekwesili tace Amurka ta taba cewa akwai tasirin Gwamnati a harkar Jami’ar.
KU KARANTA: 2019: Atiku ya samu goyon baya daga wasu Matasan Arewa
Ezekwesili tace binciken da Amurka tayi a 2005 ya nuna cewa ana zargin Atiku yana amfani da ofishin sa wajen tafiyar da harkokin wannan Makaranta don haka ake tunanin cewa Jami’ar za ta iya sukurkucewa da zarar ya bar karagar mulki.
Ministar ta Obasanjo tace tun daga lokacin ne ta tsinke da lamarin Atiku don haka take mamaki idan ta ji ana maganar zai gyara kasar nan. Mista Ezekwesili tayi wannan jawabi ne a karshen watan jiya a shafin ta na sanadarwa na zamani na Tuwita.
Jiya kun ji cewa Bola Tinubu yace Jam’iyyar APC ba ta jin tsoron shirin Atiku a 2019. Yanzu haka dai Atiku Abubakar yana Birnin Dubai inda yake tsara yadda zai doke Shugaba Buhari a zabe mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng