Salin Alin Shugaba Buhari zai yi nasara a zaben 2019 - Sanata Bukar Abba
Sanatan jihar Yobe ta Gabas, Sanata Bukar Abba Ibrahim, ya bayyana cewa salin alin kuma cikin kwanciyar hankali shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi nasarar a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya yayin babban zabe na 2019.
Sanata Bukar ya bayyana hakan ne yayin mayar da martanin wani kalami da yake dangantuwa zuwa gare shi kan cewa shugaba Buhari ba zai yi nasara ba a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya yayin babban zabe na badi.
Rahotanni sun bayyana cewa Sanatan ya yi wannan furuci ne yayin bikin kaddamar da sabon littafinsa cikin babban birni na tarayya a karshen makon da ya gabata.
Sai dai cikin wata sanarwa da sanadin kakakinsa Yusuf Ali, Sanatan na jihar Yobe ya bayyana cewa salin alin kuma cikin kwanciyar hankali shugaba Buhari zai lashe zabe yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Asali: UGC
Sanatan yake cewa, "matukar ina raye ba bu wani shamaki tsakanin shugaba Buhari da nasara a jihohin Bauchi, Yobe, Adamawa, Borno da kuma Taraba. Ba bu ta yadda za a yi Buhari ya yi rashin nasara cikin wannan jihohi a yayin babban zabe."
Dattijon na jihar Yobe ya kuma jaddada cewa, alakarsa da jam'iyyarsa ta APC tamkar takalmin Kaza ne da ba bu abinda zai shiga tsakani face Mutuwa.
KARANTA KUMA: Cibiyar Haure ta Duniya ta yaso 'Yan Najeriya 141 daga Kasar Libya
Kazalika Sanatan ya yi bugun gaba tare da alfahari dangane da yadda taka rawar gani wajen kafuwar jam'iyyar APC tun fil azal domin ceto kasar nan daga kangin cuzguni na jam'iyyar adawa ta PDP.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a daren jiya na Laraba mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sake jagorantar zaman majalisar tattalin arziki a fadar shugaban kasa dangane da dambarwar mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng