Allah ya yi: 'Yan sanda sun ceto wasu mutane 2 daga hannun ma su garkuwa a Zamfara

Allah ya yi: 'Yan sanda sun ceto wasu mutane 2 daga hannun ma su garkuwa a Zamfara

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta kubutar da wasu mutane biyu da ma su garkuwa da mutane su ka sace a garin Dansadau da ke karkashin karamar hukumar Maru.

Hukumar ta kubutar da mutanen ne a jiya, Talata, 30 ga watan Oktoba bayan an sace su tun ranar 24 ga wata.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewar tuni mutanen da aka kwato sun sadu da iyalansu. Sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansa kafin a ceto mutanen ba.

"A ranar 24 ga watan Oktoba, da misalin karfe 8:35, wasu da ake zargin ma su garkuwa da mutane ne sun sace Shehu Dangwani a kauyen Mashayar Zaki da ke masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru da Lawali Kotorkoshi a karamar hukumar Bungudu, dukkan su maza ne.

Allah ya yi: 'Yan sanda sun ceto wasu mutane 2 daga hannun ma su garkuwa a Zamfara
'Yan sanda sun ceto wasu mutane 2 daga hannun ma su garkuwa a Zamfara
Asali: Twitter

"Tun bayan samun rahoton satar su, DPO din karamar hukumar Maru ya hada wata tawagar jami'an 'yan sanda da ragowar jami'an tsaro domin a nemo su. A sakamakon tsananta bincike ne mu ka yi nasarar gano mutanen biyu a ranar 30 ga wata da misalin karfe 5:30 na yamma, an tserar da su cikin koshin lafiya," a cewar DSP Shehu.

DUBA WANNAN: Alkawarin da Buhari ya yiwa 'yan takarar APC da su ka fadi a zaben cikin gida

Kazalika, a wani labarin mai alaka da wannan a jihar ta Zamfara, jami'an tsaro na hadin gwuiwa sun dakile wani harin yunkurin satar shanu a kauyen Gungulawa da ke daf da Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

A cewar hukumar 'yan sanda, duk da ba a kama ko daya daga cikin wadanda su ka kai harin ba, ba a samu asarar rai ba kuma tuni aka mayar da shanun ga ma mallakansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng