Shekaru hudu yana damfarar mutane kan cewa shi manjo ne a soja, yanzu yazo hannu

Shekaru hudu yana damfarar mutane kan cewa shi manjo ne a soja, yanzu yazo hannu

- Hukumar yan sandan jihar Delta ta kama sojan gona

- Yayi shekaru yana amsa sunan manjo

- An kama shi ne yayin da yaje karbo wani daga ofishin yan sanda

Shekaru hudu yana damfarar mutane kan cewa shi manjo ne a soja, yanzu yazo hannu
Shekaru hudu yana damfarar mutane kan cewa shi manjo ne a soja, yanzu yazo hannu
Asali: Facebook

Hukumar yan sandan jihar Delta ta kama wani sojan gona. Ana zargin M. Sali ne da amsa manjon soja na tsawon shekaru hudu a Warri da makwafta.

Jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar, DSP Andrew Aniamaka shi ya tabbatar da hakan.

Ya bayyana cewa an kama Sali ne a ofishin yan sandan Eburumede da ke karamar hukumar Okpe lokacin da yaje da bukatar a saki wani kamammen a ofishin su.

DUBA WANNAN: Yadda za'a yi da 'yan shia

Sojan bogin, wanda bai San cewa jami'an tsaro na sane da takun shi ba, ya musa zargin da ake mishi bayan da sojoji suka yi caa a kanshi a ofishin yan sandan.

Majiyar mu ta sanar damu cewa sojan bogin ya na bayyana cewa yana cikin sojin Najeriya ne da aka tura su yankin Niger Delta.

DSP Aniamaka, yace a halin yanzu maganar na hannun bangaren binciken ta'addanci domin cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng