Da duminsa: An sace kansiloli biyu a Katsina
Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya bayyana cewar an sace wasu kansiloli biyu na karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina.
Kansilolin dai sune Hussaini Wanzam mai kula da harkokin kudi da kuma Bishir Dan Jikko mai kula da harkokin uwa da tsaftace muhalli.
Majiyar Legit.ng Hausa ta gano cewar an sace su ne a hanyarsu ta zuwa Batsari bayan sun taso daga aiki a jiya.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Jigo a APC ya yi murabus bayan ya zargi gwamnati da almundaha
Kawo yanzu, wadanda suka sace su basu bukaci a biya su kudin fansa ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng